H.E Abba K Yusuf yakai ziyarar gani da ido babban masaukin Alhazai na jihar kano

Описание к видео H.E Abba K Yusuf yakai ziyarar gani da ido babban masaukin Alhazai na jihar kano

Ayammacin wannan rana ta juma’a Mai Girma Gwamnan jihar Kano H.E Abba K Yusuf yakai ziyarar gani da ido babban masaukin Alhazai na jihar kano inda yaje domin ganewa idansa irin halinda wannan masauki yake ciki duba da yadda gwamnatin data gabata tai wasarai rai da wannan guri hasalima yadda ta cefanar da wasu guraran tareda wasu filaye dake wannan guri mai Albarka.
Adadai wannan guri yanada gidajen Alhazai kimanin 130 da ban dakuna 65, inda ahalin yanzu ko gida 1 babu awannan guri, haka bandakunan ko 15 basukai ba, saboda duk sun keta gurin sun cefanar dashi.

Akarshe mai girma Gwamna yayi alkhawarin dawowa da wannan hukuma muhallinta wanda take dashi tareda Alkhawarin zaiyi dukkan mai yuwuwa dan ganin anfarantawa mahajjatan jihar Kano duk da dai lokacin tashinsu ya karato.

02/06/2023.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке