Najeriya a 1903: Yadda Ingilishi su ka ci Kano da Sokoto, su ka kashe Sarkin Musulmi Attahiru I

Описание к видео Najeriya a 1903: Yadda Ingilishi su ka ci Kano da Sokoto, su ka kashe Sarkin Musulmi Attahiru I

A ranar Fabrairu 3, 1903 Ingilishi suka ci Kano da yaƙi lokacin Sarki Alu ya tafi Sokoto.
A ranar Fabrairu 27, 1903 arnan ƙabilar Lala suka kashe Lamiɗon Adamawa Zubairu wanda Turawa suka kora daga Yola tun cikin 1901.
A ranar Maris 15, 1903 Ingilishi suka ci Sokoto inda suka kawo ƙarshen Daular Usmaniyya.
A ranar Maris 28, 1903 Katsina ta miƙa wuya ga mulkin Ingilishi.
A ranar Afrilu 3, 1903 Gwamna Lugard ya naɗa Abbas ya zama Sarkin Kano na farko a ƙarƙashin mulkin Turawa.
A ranar Afrilu 7, 1903 Gwamna Lugard ya naɗa Alu ɗan Sidi Sarkin Zazzau bayan tuɓe Sarki Muhammadu Kwasau.
A ranar Afrilu 14, 1903 Ingilishi suka mayar da Sarkin Sudan na Kontagora Ibrahim Nagwamatse kan karagarsa shekaru biyu bayan sauke shi.
A ranar Yuli 27, 1903 Dakarun Ingilishi suka kashe Sarkin Musulmi Attahiru I a garin Mburmi.
A ranar Agusta 12, 1903 aka fara nuna fim a Birnin Lagos.
#history, #hausa, #tarihitv, #zuwanTurawaNajeriya

Комментарии

Информация по комментариям в разработке