Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulwahab Abdallah

Описание к видео Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulwahab Abdallah

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke birnin Kano a Najeriya Sheikh Abdulwahab Abdallah ya ce surorin da ya fi son karantawa a cikin AlƘur'ani su ne suratul iklas da ihsan da kuma sajadah saboda yadda suke burge shi.

Malamin ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirinmu na musamman na Ku San Malamanku, inda ya ce hadisin da ya fi so shi ne wanda Manzon Allah ke cewa yana tare da mai sonsa ranar tashin alƙiyama.

"Wannan hadisin ko yaushe na wuce shi sai na gode wa Allah. Manzon Allah ba mu san shi ba amma a ranar tashin alƙiyama wanda yake son shi zai gan shi...wannan hadisin idan na karanta shi yana faranta min rai," in ji Sheikh Abdulwahab.

Malamin ya ƙara da cewa ranar da ta fi sanya shi farin ciki a duniya ita ce lokacin da aka karɓe shi a Jami'atu Al-Islamiyya.

Sai dai malamin ya ce: "Amma babu abin da ke sanya ni baƙin ciki irin wanda ka amincewa ya je yana yi maka zangon-ƙasa."

Malamin na addinin musulunci ya ce babu garin da yake so bayan Madina da Makkah kamar Kano.

"Ina son Kano saboda gari ne wanda za ka iya isar da saƙon da kake so na ilimi da addini, kana wanda ba ka da shi za a taimake ka," in ji malamin.

Ya ƙara da cewa akwai malamai da ɗaliban ilimi waɗanda suka waye a Kano yadda ko da mutum ya yi kuskure za su fahimtar da shi cikin hikima.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке