An ci gaba da zanga-zangar ENDSARS a Abuja

Описание к видео An ci gaba da zanga-zangar ENDSARS a Abuja

Duk da kafa sabuwar rundunar SWAT da sufeton ‘yan sandan Najeriya ya yi, an ci gaba da zanga-zangar ENDSARS a Abuja.

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Muhammad Adamu ya kafa wata sabuwar runduna da za ta maye gurbin rundunar da ke yaƙi da fashi da makami ta SARS a ranar Talata.

Sabuwar rundunar ita ce SWAT, wato Special Weapons and Tactics a Turance.

A wata sanarwa wadda mai magana da yawun 'yan sandan Najeriya Frank Mba ya fitar, ya bayyana cewa za a yi wa dakarun da za su yi aiki ƙarƙashin rundunar SWAT gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa da sauran gwaje-gwaje na asibiti domin tabbatar da cewa za su iya gudanar da wannan sabon aikin.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке