Tarihin Sa'adu Zungur

Описание к видео Tarihin Sa'adu Zungur

Malam Sa’adu Zungur shahararren mawallafin rubutattun waƙoƙi ne.
Amma ko kun san shi ne ɗan Arewa na farko da Turawan Mulkin Mallaka suka tura shi makarantar gaba da sakandire a Kudancin Najeriya?
Ko kun san shi ne ya fara kafa ƙungiyar siyasa a Arewacin Najeriya?
Ko kun san shi ne ya fara shirya zanga-zangar ƙin amincewa da manufar gwamnati a Arewacin Najeriya?
Ko kun san shi ne ɗan Arewa na farko da ya riƙe muƙami a jam’iyyar siyasa ta ƙasa?
Ko kun san shi ne ya fara kai ƙarar Bature kotu kuma ya yi nasara a kansa a Arewacin Najeriya?
Wannan jajirtaccen ɗan gwagwarmayar, ya rayu ne tsawon shekaru 43 a duniya kuma ya rasu ana saura shekaru biyu Najeriya ta samu ƴancin kai.
Kuma a hakan ma ya sha fama da rashin lafiya tsawon rayuwarsa.
Wannan ya sa bai taka rawa a cikin ƴantacciyar Najeriya ba, amma har yanzu ana ganin tasirinsa a rayuwar al’ummar Najeriya.
Saboda babban almajirinsa wanda ya jagoranci gwagwarmaryar ƴanto talakan Najeriya daga zaluncin Turawan Burtaniya da magadansu Baƙaƙen Turawa shi ne Malam Aminu Kano.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке