Tarihin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto

Описание к видео Tarihin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto

Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto shi ne Firimiyan jihar Arewa na farko kuma na ƙarshe.
Shi ne ya jagoranci gwamnatin jihar Arewa tun daga 1952 har zuwa 1966.
A wannan shekaru 14 ya aza harsashin duk wani ci gaban da ake tinƙaho da shi a yankin.
Amma fa ya gwada ƙarfin ikonsa akan abokan adawar siyasa na Arewacin Najeriya.
Sannan akuyarsa ta yi kuka wurin fafatawa da ƴan siyasar Kudancin Najeriya.
A ƙarshen rayuwarsa ya mayar da hankali kan haɓaka addinin Islama da musuluntar da Maguzawa.
Kuma Sojoji ƴan tawaye sun kashe shi ranar 15 ga Janairun 1966 a juyin mulkin da bai yi nasara ba.
Sai dai, har yanzu ba a samu wani mutum da ya maye gurbinsa a Arewacin Najeriya ba.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке