Shirin Rana na DW 02.01.2025

Описание к видео Shirin Rana na DW 02.01.2025

Gwamnatin mulkin sojan a Nijar ta gabatar da kasafin kudin kasar na 2025, da ya kai na sama da biliyan dubu uku da 33 na kudin CFA.

Gwamnatin ta Nijar dai ta dauki matakan dogaro da hanyoyin samar da kudade na cikin kasar.

Hukumar Hisbah ta jihar Kano a Najeriya ta fara tattara kananan yara masu gararamba a kan tituna don mayar da su hannun iyayensu da nufin samar musu kyakkyawar tarbiyya da kuma rayuwa ta kwarai.


Masana al'amuran tsaro na ci gaba da sharhi kan ficewar sojojin Faransa daga kasar Chadi, bayan yanke alakar tsaro da kasashen biyu suka yi.

Matakin Tarayyar Turai na dauka na dakatar da cinikin gahawa da Cocoa da gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya gamu da ra’ayoyi mabanbanta. Wasu na zargin da ‘yan tawaye na amfani da abin da ake samu daga cinikin.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке