A rana irin ta yau: Janairu 04, 1967 Ojukwu da Gowon suka gana kafin Yaƙin Biafra

Описание к видео A rana irin ta yau: Janairu 04, 1967 Ojukwu da Gowon suka gana kafin Yaƙin Biafra

A ranar 4 ga Janairun 1967 shugabannin sojin Najeriya suka fara ganawa a birnin Aburi na ƙasar Ghana a yunƙurin kaucewa yaƙin basasa.
Wannan ganawar ta yini biyu, ita ce karo na farko kuma na ƙarshe da sojin Igbo suka tattauna da takwarorinsu na sauran sassan Najeriya kafin ɓalle yankinsu ya zama ƙasar Biafra.
Tun bayan juyin mulkin watan Yulin 1966, wanda hafsoshin Arewa suka ɗauki fansa kan dakarun Igbo da suka kashe msusu manya a juyin mulkin Janairun 1966, ɓaraka ta kunno kai tsakanin sassan Najeriya.
Gwamnan jihar Gabas, Kanar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu yaƙi amincewa da Kanar Yakubu Gowon a matsayin shugaban mulkin sojin Najeriya.
Har ma ya fara shirye-shiryen fitar da jiharsa daga Najeriya tare da kafa ƙasar Biafra.
Kafin akai ga haka ne aka yi ta ƙoƙarin tattaunawa domin sasanta matsalar da samun fahimtar juna.
Amma Ojukwu ya ƙi amincewa ya gana da Gowon, saboda a cewarsa babu inda yake da yaƙinin samun tsaro a Najeriya sai dai a cikin jiharsa.
Su kuma mashawartan Gowon suka ce ba daidai bane shi da yake shugaba, a ce shi ne zai tafi wurin Ojukwu neman sulhu.
Don haka aka yi cirko-cirko ana neman mafita yayin da rikici ke ci gaba da tsamari tsakanin Igbo da sauran al’ummar Najeriya.
A kan haka ne, gwamnatin Burtaniya ta bayar da wani jirgin ruwanta dake gaɓar teku a Legas, amma Ojukwu ya ce ita ma bai yarda da ita ba.
Daga nan ne,shugaban mulkin soji na ƙasar Ghana, Janar Joseph Ankra ya gayyaci ɓangarorin biyu zuwa garin Aburi, dake ƙasarsa domin tattaunawa cikin aminci.
A rana irin ta yau ne kuma wato 4 ga Janairun 1967 aka buɗe taron.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке