A rana irin ta yau: Janairu 11, 1970 Ojukwu ya tsere daga Biafra

Описание к видео A rana irin ta yau: Janairu 11, 1970 Ojukwu ya tsere daga Biafra

A ranar 11 ga Janairun 1970, jagoran ƴan tawayen Biafra, Kanar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ya tsere daga yankin.
Wannan guduwar da ya yi ita ce ta kawo ƙarshen yaƙin basasar Najeriya wanda aka kwashe watanni 30 ana fafatawa.
Saɓani tsakanin Igbo da sauran al’ummar Najeriya shi ne tushen wannan yaƙi na Biafra.
Amma Kanar Ojukwu shi ne ya zama kanwa uwar gami wurin tabbatar da yaƙin.
Shi dai Ojukwu ɗa ne ga Cif Louis Ojukwu wanda a zamanin mulkin mallaka shi ne yafi kowa kuɗi a Kudancin Najeriya.
Samun kwatankwacinsa a Arewa sai dai Alhaji Alhassan Ɗantata.
Mahaifinsa ya kai shi Ingila karatu tun daga Sakandire har zuwa Jami’a.
Don haka ya zama mutum na farko a tarihin sojin Najeriya wanda yake da digiri.
A watan Janairun 1966 lokacin da yake matsayin Laftanar Kanar kuma kwamandan rundunar sojin Najeriya dake Birnin Kano, wasu hafsoshi ƴan ƙabilar Igbo suka yi juyin mulki.
Babu hannun Ojukwu a cikin juyin mulkin, don haka bayan da manyan hafsoshin soji suka ƙwace ragamar ƙasa, sai sabon shugaban mulkin soji, Janar Aguiyi-Ironsi ya naɗa shi gwamnan jihar Gabas.
Wannan gwamnati ta Ironsi ba ta yi nisan kwana ba.
Saboda waɗanda suka yi juyin mulkin sun kashe jagororin jihohin Arewa da Yamma amma ba su kashe ƴan ƙabilarsu ta Igbo ba.
Don haka, da hafsoshin soji ƴan Arewa suka ga sabuwar gwamnati ta ƙi hukunta su, har ma ta ci gaba da fifita Igbo sai suka gudanar da juyin mulkin ɗaukar fansa a watan Yulin 1966.
Sakamakon haka ne, aka naɗa Kanar Yakubu Gowon a matsayin shugaban mulkin sojin Najeriya na biyu.
Amma Ojukwu ya ƙi yi masa mubaya’a saboda ya raina shi kuma ya na ganin ba shi ya kamata ya zama shugaban ƙasa ba.
Aka yi rashin sa’a bayan juyin mulki an ci gaba da kisan Igbo musamman a Areawcin Najeriya.
Don haka Ojukwu ya yi amfani da wannan damar ya umarci ƴan jiharsa su koma gida.
A watan Janairun 1967 Ojukwu da Gowon tare da sauran gwamnonin mulkin sojin Najeriya suka tattauna a Aburi, suka cin ma matsayar bai wa jihohi ƙarfi fiye da Gwamnatin Tarayya.
Amma bayan da suka dawo gida, manyan ma’aikatan Gwamnati suka shaidawa Gowon cewa ba zata saɓu ba.
Sakamakon wannan saɓanin, jihar Gabas ta fice daga Najeriya ranar 30 ga Mayun 1967 tare da sauya suna zuwa Jamhuriyar Biafra.
A ranar 6 ga Yulin 1967 kuma yaƙi ɓarke tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da yankin ƴan tawaye na Biafra.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке