Shirin Rana na DW

Описание к видео Shirin Rana na DW

A Najeriya kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ce ta nuna damuwa da karuwar cin zarafin ‘yan mata a kasar, kama dag wadanda ake garkuwa da su da wasu a makarantu har da wasu da ake yi a cikin al’uma.

Gwamnatin soja a Nijar ta kwace takardar izinin zama dan kasa na wasu 'yan kasar da ke goyon bayan hambararriyar gwamnatin Shugaba Bazoum Mohamed. Matakin ya shafi fararen hula da sojoji wadanda gwamnatin ke zargi da laifuka ciki har da hada baki da wasu kasashen waje wajen neman kawo wa Nijar hari.
Matsalar tsaro ta tilasta wa dubun dubatar mutane yin hijira daga Burkina Faso sun kaurace wa gidajensu tare da samun mafaka a yankunan arewacin Côte d'ivoire mai makwaftaka da kasar.
Akwai kuma sharhunan jaridun Jamus kan harkokin da suka shafi kasashen Afirka da muka saba kawo muku a ranakun Juma’a.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке