Waiwaye kan munanan hare-haren da Shekau ya jagoranta a shekara 12

Описание к видео Waiwaye kan munanan hare-haren da Shekau ya jagoranta a shekara 12

Shekara ɗaya bayan mutuwar shugaban ƙungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ana ta samun ƙaruwar ƴaƴan ƙungiyar da ke mika wuya ga sojojin Najeriyar.

Tun bayan mutuwar jagoran ƙungiyar ake ganin lagon ƙungoyar ya karye, kuma ruɗani ya kutsa cikinta, har wasu daga cikin ƴaƴanta da jigoginta suka shiga miƙa wuya ga sojojin Najeriya.

A ranar 19 ga watan Mayun 2021 ne aka fara samun labarin mutuwar Abubakar Shekau, mutumin da ya shafe shekara 12 yana jan ragamar kungiyar masu tayar da ƙayar baya ta Boko Haram, wacce ta dinga kai munanan hare-hare a Najeriya da Nijar da Kamaru har ma da Chadi.

A yayin da yake cika shekara daya da barin duniya, BBC Hausa ta yi waiwaye kan wasu munanan hare-hare 12 da Shekau ya jagoranta cikin 12 da ya yi yana jan ragamar ƙungiyar, waɗanda suka daga hankula a duniya.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке