Shirin Rana na DW 10.07.2024

Описание к видео Shirin Rana na DW 10.07.2024

Shirin Rana
- Kungiyoyin makiyaya da manoma a Najeriya sun nuna gamsuwarsu da matakin gwamnatin tarayyya na assasa ma’aiakata da za ta kula da bunkasa harkar kiwo domin magance matsalolin rigingimun da ake samu tsakaninsu.
- Al'ummar jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya na tsokaci kan aikin jin-kai da 'yan kasuwar shinkafa a garin Argungu da ke jihar Kebbi suke yi, na rage farashin shinkafa domin tausaya wa marasa karfi.
-A Jahuriyar Nijar, kamfanin ORANO na kasar Faransa ya sanar da fadawa matsalar rashin kudaden shiga da na gudanarwa a kamfanin SOMAYIR da ke zama daya dayan kamfanin uranium na Nijar da ya yi saura wanda Faransa ke da hannun jari a cikinsa.
-Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embaló ya isa kasar China don fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku, da yake fatan za ta kara karfafa alakar ciyar da kasarsa gaba.
Da fatan za a kasance da mu.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке