Karin aure yana nan daram ba gudu ba ja da baya - Malam Alkali Abubakar Salihu Zaria

Описание к видео Karin aure yana nan daram ba gudu ba ja da baya - Malam Alkali Abubakar Salihu Zaria

Shehin Malamin nan Alkali Abubakar Salihu Zaria ya ce yawan yabon da ya ke yiwa uwargidansa Jamila ba zai hana shi auren Sumayya ba.
A wata hira da Freedom Radio, ya ce auren da zai kara zai ragewa Jamila ayyukan gida sannan idan Allah ya amshi ransa ba ita kadai za ta ji zafi ba, haka kuma idan ita ta riga shi zai samu saukin radadi.
Ya ce, masu rubuce-rubuce kan aurensa a Social Media su sani babu abin da zai canja kuma ita Jamila kishinta irin wanda shari’a ta yarda da shi ne.
Malamin ya kuma ce, yabon da yake wa Hajiya Jamila yana nan daram ko gobe, haka ma karin auren mutuwa ce kawai za ta hana.
Freedom Radio ta tambayi Malamin ko daga Sumayya an rufe kofa?
Za kuji amsar da Malam ya bayar.
Muma daga nan Muryar Jama’a Muna yiwa Malam Fatan Alkhairi, Allah ya bada zaman lafiya.

Комментарии

Информация по комментариям в разработке